Bello Turji
Ana zargin yaran Bello Turji sun kai hari a wani yanki na Shinkafi a jihar Sokoto. Sun kashe wani matafiyi Yusuf Isah kafin dakarun soji Najeriya su fatattake su.
Mai fashin baki kan lamuran tsaro, Alhaji Sani Shinkafi ya ce tattaunawar da aka yi da Bello Turji ba ta da amfani, inda ya bayyana ta a matsayin rashin adalci.
Yayin da ake maganar haɗaka da Bello Turji, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya bayyana damuwa kan yadda ta'addanci ke kara ta'azzara musamman a yankin Arewa.
Jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji ya sanar da ajiye makamai bayan zaman sulhu da aka yi da shi a Zamfara. Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah ne ya sanar da haka.
Babban malamin Musulunci a Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya sake bayyana damuwa kan ta'addanci yana mai jaddada yin sulhu da su Bello Turji.
Masanin tsaro, Sani Shinkafi ya zargi gwamnatin tarayya da dakile yunkurin kama Bello Turji ko kashe shi a Zamfara duk da cewa CJTF sun kusa gamawa da shi.
Gwamnatin jihar Sokoto ta yi magana kan sulhu da ake shirin yi da yan bindiga bayan munanan hare-haren da ake kai wa inda ta gindaya sharuda ga Bello Turji.
Hatsabibin dan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya Bello Turji ya saki sabon bidiyo ana cikin maganar sulhu inda ya ce yana tattaunawa da gwamnati.
Raoto ya gano cewa dan ta'adda Bello Turji na neman ajiye makamai ne domin ganin karfinsa ya kare bayan kashe dan ta'adda Danbokolo da 'yan sa-kai suka yi.
Bello Turji
Samu kari