Bello Turji
Yayin da Janar Christopher Musa ya bar ofis ba tare da cika alkawarin da ya dauka ba, Bello Turji ya ci gaba da zama tushen kalubalen tsaro a Arewacin Najeriya.
Jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji ya saki sama da mutum 100 a kokarin kawo zaman lafiya a Najeriya. Ana kokarin sulhu da Turji domin daina kai hare hare Zamfara.
Bello Turji ya fara shirya sababbin hare-hare a gabashin Sokoto bayan ruwan damina ya ja baya, an ce ya sake tsara runduna da sauya kwamandoji don karfafa iko.
Al'ummar garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina sun kama wasu da ake zargin yan bindiga ne wadanda ke kai hare-hare yankunansu ba kakkautawa.
Dan ta'adda a Arewacin Najeriya, Bello Turji ya yi magana kan sulhu da ake magana inda ya ce kowa na son zaman lafiya duba da shi ne hanyar ci gaba.
A labarin nan, za a ji cewa wani ɗan bijilanti ya bugi ƙirji, ya ce zai iya kamo Bello Turji da ake tsammanin ya gagari rundunonin tsaron kasar nan.
Maganar sulhu na ci gaba da jawo magana a Arewacin Najeriya inda wasu malaman Musulunci suka rarrabu kan lamarin yayin da wasu ke cewa sulhu ne mafita.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan ko ya dace a yi sulhu da yan bindiga ko a'a, al’ummomi a wasu yankunan jihar Zamfara da Sokoto sun bayyana matsayarsu.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bukaci a yi watsi da sulhu da Bello Turji ya ce zai yi da gwamnati. Ya bukaci a kashe dan ta'addan.
Bello Turji
Samu kari