Bayelsa
Ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya lashe zaɓen gwamna a ƙaramar hukumar Brass ta jihar.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta dakatar da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Bayelsa. An bayyana jerin ƙananan hukumomin da APC, PdP suka lashe.
Wasu da ake zargin ƴan bangar siyasa ne sun halaka wani mai goyon bayan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a cibiyar tattara sakamakon zaɓe a Bayelsa.
Hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya (INEC) ta tabbatar da cewa an tsare wasu jami'anta a karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa ba tare da son ransu ba.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da kuɓutar da aka sace ana jajibirin zaɓen gwamnan jihar Bayelsa na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
Bayan ayyana sakamakon zabe a kananan hukumomin Kolokuma/Opokuma, Ogbia da Yenagoa, hukumar INEC ta dage ci gaba da tattara sakamako zuwa karfe 3 na yamma.
Jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasararta ta farko a jihar Bayelsa a karamar hukumar Gwamna Duoye Diri yayin da INEC ta fara tattara sakamakon karshe.
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun farmaki wasu rumfunan zabe a jihar Bayelsa, inda suka sace kayayyakin zabe bayan bude wuta.
Bayanai da suke fitowa sun nuna cewa Hukumar Zabe mai Zaman Kanta (INEC) za ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan Kogi da Bayelsa gobe Lahadi 12 ga watan Nuwamba.
Bayelsa
Samu kari