
Jihar Bauchi







Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ya sanar da rasuwar kawunsa kuma Sarkin Alkaleri, Alhaji Muhammadu Abdulkadir, wanda ya rasu yana da shekaru 100.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya kai ziyara domin yin ta'azziya ga gwamnan Filato, Caleb Mutfwang bayan rasuwar Sheikh Sa'id Hassan Jingir.

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bayyana cewa duk wanda zai tsula tsiya a nan duniya, ya sani cewa babu makamawa akwai ranar da Allah zai masa hisabi.

Yayin da gwamna Bala Mohammed zai kammala mulkinsa a 2027, Sanata Ahmed Abdul Ningi ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Bauchi a 2027 karkashin PDP.

Ministan lafiya, Ali Pate ya ce yana da burin yin takarar gwamnan Bauchi a 2027, amma yanzu ya mayar da hankali kan aikin da Shugaba Tinubu ya ba shi.

Omoyele Sowore ya soki rufe makarantu a Arewa yayin Ramadan, yana mai cewa matakin jahilci ne, kuma a Saudiyya ba sa yin hakan domin ilimi ya fi muhimmanci.

Majalisar Shira ta tsige shugaban karamar hukumar, Abdullahi Beli, da mataimakinsa bisa zarge-zargen rashawa. An nada Hon. Wali Adamu a matsayin mukaddashi.

Gwamnatocin Arewa sun yi martani ga kungiyar kistoci kan rufe makarantu a Ramadan. Za a rufe makarantu a Kano, Kebbi da Bauchi duk da korafin CAN.

Safiyanu Dalhatu ya kashe mahaifiyarsa da tabarya a Bauchi. Yanzu dai 'yan sanda sun kama shi, sun kwace makamin, kuma ana shirin gurfanar da shi a kotu.
Jihar Bauchi
Samu kari