Atiku Abubakar
Tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi sun bayyana fatan Najeriya za ta bunkasa a sabuwar shekarar 2025 da aka shiya a ranar Laraba.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fito ya yi magana kan batun da aka rika yadawa kan cewa ya cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku Abubakar da Peter Obi.
An bayyana yadda manyan siyasa a Najeriya ke shirin tabbatar da sun kwace mulki a hannun Bola Ahmad Tinubu a zaben shugaban kasa da ke tafe a nan da 2027.
An yada wani faifan bidiyo inda matashi ya bayyana nadamarsa kan rashin goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023, yana mai cewa ya yi kuskure.
Wani jigo a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya bukaci ka da a tsayar da dan Arewa takara a zaben shugaban kasa na 2027. Ya hango matsala idan aka yi hakan.
Jigo a siyasar Kudancin Najeriya, Doyin Okuoe ya ce bai kamata wani dan Arewa kamar Atiku Abubakar ya karbi mulki a hannun shugaba Bola Tinubu ba a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi rashin tsohon hadiminsa, Hon. Shima Ayati wanda ya rasu a Makurdi bayan gajeriyar rashin lafiya.
Atiku Abubakar ya ce gibin Naira tiriliyan 13 a kasafin 2025 yana nuna rashin tsari mai dorewa da dogaro kan bashi, yana kira da rage kashe kudin gwamnati.
Atiku Abubakar ya jajanta wa iyalai kan turmutsitsin da ya yi ajalin rayukan mutane a jihohin Najeriya, ya bukaci matakan tsaro don kare faruwar irin hakan a gaba.
Atiku Abubakar
Samu kari