Arewa
Jagoran jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya ce abin kunya ne yadda gwamnonin Arewa suke rufe makarantu saboda barazanar rashin tsaro da sace dalibai da malamai.
A labarin nan, za a bi cewa wasu Katsinawa sun gaji da isar ƴan ta'adda, sun hana su kuɗin fansa, sannan sun yi garkuwa da iyalansu na yan kwanaki.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba za ta kulle makarantu ba, saboda matsalar rashin tsaro. Ta bayyana cewa ta dauki matakan da suka dace.
Masu garkuwa da mutane sun kai hari a Toro, Bauchi, inda suka kashe dan agajin Izalah, Alhaji Muhammad Bakoshi, sannan suka sace matarsa da ‘yarsa mai shekara biyar.
Rundunar ‘yan sanda ta Gombe ta karyata rahoton harin coci da sace mutane da ya yadu a kafofin sadarwa, tana cewa jami’ai sun kasance wurin tun da safe.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta yi wa Sanata Garba Maidoki martani. Ta zarge shi shi da yada bayanan karya kan rashin tsaro.
Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki matakin rufe dukkanin makarantu na gwamnati da na kudi saboda rashin tsaro. Ta ce za ta sanar da ranar da za a koma.
Sanatan Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, Garba Maidoki ya bayyana bakin cikinsa kan sace dalibai a Maga a jihar yana cewa lamarin ya taba masa zuciya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya damu matukan kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce gwamnatinsa na daukar matakai.
Arewa
Samu kari