Arewa
Gwamnonin jihohin Arewa sun gudanar da taro kan matsalar rashin tsaro. Sun samo hanyoyin da suke son abi domin kawo karshen matsalar da ta addabi yankin.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bukaci gwamnatocin yankin Arewacin Najeriya da su kasance masu sauraron jama'a.
Gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya sun shiga ganawa kan matsalolin rashin tsaron da ake fama da su a yankin. Za su tattauna don samun mafita.
Cibiyar Zakkah da Wakafi a jihar Gombe, karkashin Dr Abdullahi Abubakar Lamido ta ba matasa kusan 100 horo a shirinta na shekara shekara na 2025.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a sabon cocin da aka gina kwanakin nan a garin Ejiba, da ke karamar hukumar Yagba West, inda mazauna suka shiga firgici.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna damuwa kan matsalolin rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce lissafo abubuwan da ke rura wutar matsalar.
Rundunar ‘yan sandan Kogi ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun sace mutane biyu yayin da mutum daya ya tsere a harin da suka kai kan hanyar Isanlu zuwa Idofin.
Daga cikin sunaye mutane 35 da Tinubu ya aike wa majalisar dattawa domin tantancewa matsayin jakadu, an gano cewa mutane 15 sun fito ne daga Arewacin Najeriya.
Kungiyar Diocese ɗin Katolika ta Kontagora ta fitar da sunayen mutum 265 — malamai, ma’aikata, daliban sakandare da firamare — da har yanzu suke hannun ’yan bindiga.
Arewa
Samu kari