Arewa
A labarin nan, za a ji cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya shaida cewa yawan alkawura babu aiki da shugabanni ke yi ba zai haifar da da mai ido a Arewa ba.
Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwa cewa Shugaba Tinubu zai samu karin kuri’un Arewa a 2027 musamman a Arewa maso Yamma saboda tsaro ci gaba.
Babbar kotun jihar Filato ta gamsu fa bayanan Fatima Baba da mahaifinta, ta amince cewa duk Bahaushen da aka haifa a Jos ta Arewa dan asalin yankin ne.
Mamakon ruwan sama tare iska mai karfi ya jawo ambaliya da ta yi sanadin mutuwar wata mata da jikarta a jihar Bauchi. Rahoto ya nuna irin barnar da ruwan ya yi.
Kungiyar dattawan Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro, tana cewa Najeriya na fuskantar mummunar barazana.
Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma sun fara aiwatar da tsare-tsaren hadin gwiwa domin rage talauci ta hanyar fadada shirye-shiryen kariyar zamantakewa.
Akalla mutum 10 sun jikkata bayan rikici ya barke tsakanin al’ummomin Chirif Magaji da Chirif Dikko a karamar hukumar Rabah ta jihar Sokoto kan rikicin gona.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta bayyana shirin da ta fara wajen tabbatar da lafiya masoya 3,000 da suka shiga shirin auren gata.
Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume ya bayyana cewa yan Arewa maos Gabas za su saka wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kuri'insu bisa aikin titin Gombe zuwa Biu.
Arewa
Samu kari