Arewa
Bayan faruwar iftila'in harin bam da sojoji suka yi, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'azziyarsa bayan rasuwar mahaifiyar Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa da dansa a wannan mako.
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya kwanta dama, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya ranar Alhamis.
Bello Turji ya sake yin sabon bidiyo inda ya soki hukumomin Najeriya da sojoji kan yada cewa an kama wasu daga cikin yan uwansa da suka mataimakansa ne.
Gwamnan Bauchi, Bala Abdulƙadit Mohammed ya ce kafewar shugaban ƙasa Bola Tinubu kan kudirin haraji gayyato rikici ne, ya ce tsarin ba alheri ba ne.
Gwamna Ahmed Aliyu ya nada sababbin shugabanni don inganta gwamnati, yana mai jaddada gaskiya da adalci tare da tabbatar da ribar cigaba ga dukkan jama'a.
Hukumomi a Karamar Hukumar Garun Malam a jihar Kano sun rufe Kasuwar Tumatur ta Kwanar Gafan saboda zargin ayyukan fasadi, karuwanci da wasu munanan dabi'u.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa da yawa daga cikin waɗanda suka kaɗa masu kuri'a suna fama da wahalhalun rayuwa a yanzu.
Wasu mazauna yankunan Idi da Ranbadawa a jihar Sokoto sun nemi gwamnati ta tsare su daga zaluncin Kallamu, wani fitaccen dan bindiga mai alaka da Bello Turji.
Arewa
Samu kari