Arewa
Kungiyar Kiristoci a yankin Arewa maso Yamma ta nuna damuwa kan yadda aka yi wariya a mukaman hukumar raya yankin Arewa maso Yamma (NWDC) kan nadin mukamai.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau ya umarci wani basarake ya sauka daga mukaminsa domin gudanar da bincike wanda wata kungiya ta kalubanci matakin.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa bayan mutuwar mutane a iftila'in hatsarin jirgin ruwa dauke da masu bikin Maulidi a jihar Niger.
Kungiyar ACF ta bayyana damuwa kan karuwar rashin tsaro a sassan Arewacin kasar nan, inda ake ganin lamarin zai kazanta idan ba a dauki mataki a na gaba ba.
Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta amince da sayen jami'ar Khadija kan Naira biliyan 11, za a biya kuɗin a kashi uku.
A wannan labarin, za ku ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar talauci a Arewacin kasar nan duk da karuwar arzikin kasa.
Jam'iyyar NNPP da ke karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta rasa jiga-jiganta zuwa jam'iyyar APC da Abdullahi Ganduje ke shugabanta.
Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idirs Kauran Gwandu ya bai wa sarakuna 4 masu daraja ta ɗaya kyautar motocin alfarma irin wsɗanda yake hawa, ya yaba masu.
Hasashen yanayi da hukumar NiMet ta fitar a ranar Talata a Abuja ya nuna cewa za a zabga ruwa da tsawa a sassan jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, Kebbi, da sauransu.
Arewa
Samu kari