Arewa
Adadin mutanen da suka mutu a fashewar tankar mai da ta afku a garin majiya, karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa ya kai 180. Mazauna garin sun yi karin bayani.
Kungiyar Kuteb Muslim Development Association (KMDA) ta yi magana kan zargin shirin rushe masallacin Juma'a inda ta shawarci Gwamna Agbu Kefas na Taraba.
Rikicin cikin gida na jam'iyyar APC a jihar Sokoto ya sake dagulewa kan wanda zai jagorance ta tsakanin Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido.
Shugaban gwamnonin Arewa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa al'ummar jihar Jigawa kan iftila'i da ya afku inda suka ba da gudunmawar N900m.
Wasu yan siyasa masu ƙarfin fada a ji a yankin Arewacin Najeriya suna kokarin neman yardar Jonathan domin tsayawa zabe a 2027 saboda dakile Bola Tinubu.
Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wasu tsageru suka yi awon gaba da mutane tare da kashe wasu 'yan sa kai a wani yankin jihar Katsina da ke Arewa.
Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike domin dawowa da marayu hakkinsu da aka danne a jihar Kebbi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar Hisbah a Kano ta kama wani kwamishina daga jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara kan zargin lalata da matar aure.
Hedkwatar tsaro ta ƙasar nan watau DHQ ta baygana cewa sojoji sun sheke ƴan ta'adda 96, sun cafke wasu sama da 200, tare da ceto mutanen da aka sace a mako 1.
Arewa
Samu kari