Arewa
Sabuwar kungiyar Lakurawa da ta bulla a Sokoto ta fara karfi a kananan hukumomi biyar da ke jihar inda suka fara karbar Zakka daga al'ummar yankunan.
Malam Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ta dura kan Gwamnan Bala Mohammed na Bauchi kan take hakkin al'umma inda ya ce shi ma dan Adam ne lokacin da aka ci zarafinsa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai sallami kwamishinoni da ba su tabuka komai ba domin kawo wasu sababbin jini.
An zargi jami'an NDLEA da kashe Faisal Yakubu Hussaini a Dangi, jihar Filato, yayin da suka kai samame a gidan saukar baki. Hukumar ta yi martani kan wannan zargi.
Kamfanin rarraba hasken lantarki na kasa (TCN) ya ce za a cigaba da samun matsalar rashin wuta har na tsawon lokaci kafin ya dawo yadda ya dace a kasar nan.
Gwamnatin Kaduna na shirin zuba N93 biliyan cikin shekaru hudu don gyara sashen ruwa, magance jahilcin da ya shafe shekaru goma, da inganta KADSWAC har zuwa 2027.
An gurfanar da Bala Muhammed, dattijon nan na Bauchi da ya rika wallafa hotunansa da 'yan mata a Facebook. Ana tuhumarsa da bata sunan wadda ta yi kararsa.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana wasu mutum tara da take nema ruwa a jallo a Arewa maso Gabas kan zargin ta'addanci da rikau, ta lissafo sunayensu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane 22 ne suka ce ga garinku nan yayin da wani ramin haƙar ma'adanai ya rufta kansu a yankunan Adamawa, Taraba.
Arewa
Samu kari