Arewa
Gwamnatin jihar Kebbi ta dauki matakin rufe dukkanin makarantu na gwamnati da na kudi saboda rashin tsaro. Ta ce za ta sanar da ranar da za a koma.
Sanatan Kebbi ta Kudu a majalisar dattawa, Garba Maidoki ya bayyana bakin cikinsa kan sace dalibai a Maga a jihar yana cewa lamarin ya taba masa zuciya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya damu matukan kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce gwamnatinsa na daukar matakai.
Gwamna Zulum ya umurci mazauna Borno su gudanar da azumi da addu’a a Litinin domin neman taimakon Allah kan sabon tashin hankali da ake fuskanta a jihar.
Wannan rahoto ya yi nazari kan yadda jihohi 6—Borno, Yobe, Zamfara, Plateau, Benue da Katsina—ke amfani da sababbin dabarun tsaro wajen yaƙi da ‘yan ta'adda.
Allah ya yi wa matar Sarkin Suleja, Malam Muhammad Awwal Ibrahim rasuwa. Marigayi Hajiya Rahmatu Awwal Ibrahim ta yi bankwana da duniya ne bayan ta yi jinya.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Neja ta la’anci harin da ‘yan bindiga suka kai St. Mary’s Papiri, inda aka sace dalibai, malamai da ma’aikacin tsaro.
Gwamnatin Katsina karkashin Gwamna Dikko Radda ta rufe makarantun firamare da sakandire a fadin jihar saboda dalilai na tsaro bayan farmakin da aka lai Neja.
Tsohon ministan sadarwa, Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami, ya koka kan hare-haren da aka yi fama da su a wasu sassan kasar nan. Ya bukaci hukumomi su tashi tsaye.
Arewa
Samu kari