Arewa
Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da nadin dan uwan Abubakar Malami (SAN) a matsayin shugaban hukumar KEBGIS bayan ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Kungiyar hada kan 'yan Arewa ta NRG ta kai ziyara ga shugabannin Musulmai da Kiristoci na JNI da CAN domin kara fahimtar juna a Arewacin Najeriya.
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago, ya fatattaki masu bashi shawara na musamman har su 30 domin sake tsara gwamnati da karfafa ajandar 'sabuwar Neja'.
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya ce babu hannunsa a daukar nauyin ta'addanci, ya ce zargin da Bello Turji ya yi a kansa ba gaskiya ba ne.
Jam'iyar APC reshen jihar Zamfara ta bayyana cewa abubuwan da Bello Turji ya fada sun nuna karara cewa Bello Matawalle ba shi da alaka da 'yan bindiga.
A cikin wani bidiyo, Bello Turji ya zargi tsofaffin gwamnonin Arewa biyu da haddasa rashin tsaro, yana musanta karbar N30m a tattaunawar zaman lafiya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa sabuwar runduna ta musamman wadda za ta rika kula da tashoshin motoci da sauran wuraren da jama'a ke taruwa.
Shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar da NLC ke shirin yi a fadin ƙasar a ranar 17 ga Disamba.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta sanar da rasuwar mataimakin kwamishina mai kula da ayyuka, DCP Kabiru Audu wanda ya bar duniya bayan jinya mai tsawo.
Arewa
Samu kari