Yaki da rashawa a Najeriya
Dakarun 'yan sanda dauke da manyan makamai sun kama tsohon shugaban hukumar PCACC ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado a ofishinsa yau Juma'a.
Hukumar EFCC ta karɓe fasfo ɗin tsohon minista, Abubakar Malami, yayin da take bincike kan badakalar $490m na Abacha da aka dawo da su karkashin MLAT.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya bayyana cewa hukumar EFCC ta tura masa gayyata. Malami ya ce zai amsa gayyatar ba tare da jin tsoro ba.
Babbar kotun Kano ta dage shari'ar zargin cin hanci da almundahana da ake wa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, matarsa, danss da wasu shida.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta dage sauraro karar da EFCC ta kai tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano har sai baba ta gani kan almundahana.
A labarin nan, za a ji cewa Ofishin Mai Binciken Asusun Gwamnati ya yi bincike, inda ya gano wasu kudi da aka yi amfani da su ba bisa ka'ida ko shaida ba.
Majalisar dokokin jihar Kebbi da ke Arewacin Najeriya ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai, Muhammad Mahuta bisa zargin aikata rashin gaskiya.
EFCC ta ayyana tsohon ministan man fetur kuma tsohon Gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin karkatar da dala miliyan 14.8.
Hukumar DSS ta kori jami’ai 115 bisa zargin rashawa da zamba, ta gargadi jama’a kan tsofaffin jami’an da ke amfani da sunan hukumar wajen cutar da mutane.
Yaki da rashawa a Najeriya
Samu kari