
Anambra







Valentine Ozigbo ya koma APC daga LP, yana neman takarar gwamna a Anambra. Bashir Ahmad ya ce jam’iyyun adawa za su rushe kafin nan da babban zaben 2027.

PDP ta fara sayar da fom ɗin takarar gwamnan Anambra, zaɓen fidda gwani zai gudana 5 ga Afrilu, yayin da za a mika sunan ɗan takara zuwa ga INEC a ranar 22 ga Mayu.

Bayan yada wasu rahotanni, Gwamnatin Anambra ta karyata jita-jitar kama mata da ba su saka rigar nono da dan kamfai a wuraren taruwar jama'a a jihar.

Al'ummar mazaɓar Onitsha a jihar Anambra sun nuna ɓacin ransu, sun soki Gwamna Charles Chikwuma Soludo kan kisan ɗan Majalisarsu da ƴan bindiga suka yi.

Wata daliba a Jami’ar UNIZIK ta ciji malami bayan sun samu sabani kan daukar bidiyon TikTok. Jami’an tsaro sun fara bincike kan don gano gaskiyar lamarin.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa (APC), Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan zaben gwamnan jihar Anambra. Ya nuna cewa lokaci ya yi da yakamata a samu canji.

'Yan bindigan da suka tafka aika-aikar kashe dan majalisar dokokin jihar Anambra, sun fitar da bayani kan ta'addancin da suka yi. Sun ce sun harbe shi sau biyu.

Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa dakarunta sun cafke mutane tara da ake zargi da hannu a kisan Ɗan Majalisar dokokin jihar Anambra, Hon. Justice Azuka.

Yan bindigar da suka sace mamban Majalisar dokokin jihar Anambra. Justice Azuka sun ƙashe shi, an gano gawarsa da ta fara rubewa a gadar Neja ta biyu.
Anambra
Samu kari