
Aikin Hajji







Gwamnatin Kano ta umarci hadiman da aka nada mukamai daban daban da su gaggauta bayyana adadin kadarorin da suka mallaka ga hukumar da'ar ma'aikata.

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta shirya fara jigilar maniyyata zuwa kasa mao tsarki domin gudanar da aikin Hajjin 2025. Za a fara jigilar bayan azumi.

Shugaban hukumar NAHCON mai kula da Alhazai ta Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh, ya sha alwashin cewa ba za su ba Shugaba Bola Tinubu kunya ba kan Hajjin 2025.

Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta fitar da sanarwa kan daukar ma'aikatan lafiya domin aikin hajjin bana. Za a fara daukar ma'aikata a ranar 8 ga watan Maris.

Rahoto ya zo cewa kusa a jam'iyyar APC, kuma tsohon kwamishina, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce yan adawa sun kullo makircin bata wa shugaban hukumar NAHCON suna.

A farkon watan Fabrairu kasar Saudiyya ta sauya dokar shige da fice wacce za ta shafi Najeriya Najeriya, Algeria, Egypt, Ethiopia, Morocco, Sudan daTunisia a Afrika.

Bayan ware miliyoyi saboda daukar nauyin Musulmi zuwa aikin hajji, wasu 'yan asalin Ebonyi sun bukaci Majalisar Dokokin jihar Ebonyi ta tsige Gwamna Francis Nwifuru.

An yi ta ce-ce-ku-ce bayan gwamnatin jihar Ebonyi ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya don aikin Hajjin 2025.

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kara wa'adin lokacin biyan kudin Hajjin 2025. Hukumar NAHCON ta bukaci maniyyata da su biya kudadensu a kan lokaci.
Aikin Hajji
Samu kari