Agboola Ajayi
Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ondo na kan gaba a sakamakon zaben gwamnan Ondo da aka sanar na kananan hukumomi 15. PDP na biye da ita a can baya.
Dan takarar gwamnan jam'iyyar APC na jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya shiga gaban na PDP bayan sanar da sakamakon zabe daga kananan hukumomi 15 na jihar.
Ana ci gaba da zaman jiran tsammani a Ondo a safiyar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba, yayin da INEC ta bayyana lokacin da za ta ci gaba da tattara sakamakon zabe.
Sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024 ya fara fitowa daga rumfunan zabe, gundumomi da kananan hukumomin jihar.
Wani jagoran APC a jihar Ondo ya ce za su samu nasara a zaben gwamna da ake gabatarwa a jihar. Dan APC ya ce babu wata jam'iyyar adawa da za ta iya ja da APC.
Dan takarar jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), Dr. Abass Mimiko, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai tsoma baki ba a zaben gwamnan Ondo.
Jam'iyyun siyasa sun ci kasuwar sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Ondo da ake yi yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024, an rika ba mutane takarda.
Rahotannin sun tabbatar da cewa yan daba sun yi ta harbe-harbe wanda ya tilasta mazauna wan yankin Ondo shigewa gidajensu saboda fargaba ana tsaka da zabe.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour (LP) a zaben Ondo Festus Ayo Olorunfemi ya kada kuri’a a zaben jihar da ke gudana. Bidiyo ya nuna lokacin da ya kada kuri'a.
Agboola Ajayi
Samu kari