Hadarin jirgi
Rahotanni sun nuna cewa wani kwale-kwale da ya ɗauko mutane akalla 200 ya kife a kogin Neja a jihar Neja, ana fargabar da mutane da dama sun rasa rayukansu.
Mutum 5 sun rasa rayukansu da wasu jiragen ruwa guda biyu suka yi taho mu gama a ƙaramar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta, wasu fasinja 20 sun ɓata.
Wani jirgin sama na kamfanin Air Peace ya yi gaggawar fasa tashi sakamakon wata tsuntsuwa da ta gutta masa a filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja yau da safe.
Jirgin saman kamfanin Air Peace ya yi wata saukar gaggawa bayan samun matsala a sama. Jirgin ya dauko mutane daga Benin na jihar Edo zuwa birnin Abuja.
Ofishin binciken tsaron Najeriya (NSIB) ya sanar da gano karin gawar mutum guda da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su da jihar Ribas. Hadarin ya afku a makon jiya.
Shugaba Bola Tinubu ya nemi a tsaurara bincike da aikin ceto yayin da ake fargabar fasinjoji takwas sun mutu a hatsarin jirgin sama da ya faru a jihar Ribas.
An samu bayanai kan matukin jirgin saman da ya yi hadari da jami'an NNPCL. Wanda haɗarin ya ritsa da shi babban ne sosai a kungiyar matuƙa jirgin sama ta kasa.
Mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa jirgin mai saukar ungulu da ya yi hatsari a Ribas mallakin kamfanin East Winds ne.
Mutane uku sun rasa rayukansu bayan jirgi mai saukar ungulu ta fadi a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers inda mutane uku suka rasa rayukansu dalilin haka.
Hadarin jirgi
Samu kari