Abun Bakin Ciki
Sojojin Nijar sun ce suna sake samun iko bayan wasu sojojin tawaye sun yi yunkurin kai hari kusa da fadar shugaban kasa a Niamey wanda aka shiga tashin hankali.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya yi wa Sarkin Bolari, Alhaji Ahmad Abubakar, rasuwa cikin daren nan bayan fama da rashin lafiya a birnin Gombe.
Shugaban hukumar kidaya ta kasa, NPC, Aminu Wushishi, ya rasu ranar Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya, yayin da abokansa da ‘yan siyasa suka shiga jimami.
An tabbatar da rasuwar babban sakataren kungiyar kwadsgo ta Najeriya, NLC, Emmanuel Ugboaja yana da shekaru 60 a duniya, ya rasu bayan doguwar jinya.
’Yan kasuwa biyar sun mutu bayan wata motar sojoji ta kwace daga hanya ta kutsa cikin kasuwa a garin Chanchangi da ke jihar Taraba, yayin da wasu suka jikkata.
Tsohon sakataren gwamnatin Oyo, Abdul Waheed Olajide, ya rasu yana da shekaru? Iyalansa sun sanar da rasuwar, inda aka shirya jana’izarsa a Ibadan.
Yan daba sun kashe matashi mai suna Yusuf Ahmad a Dorayi, Kano, bayan wani rikici da ake zargin ya samo asali daga ramuwar gayya tsakanin wasu matasa.
Akalla jarirai 15 sun mutu bayan gobara ta tashi a sashen haihuwa na asibitin PIMS da ke Islamabad, Pakistan, inda ake gudanar da bincike kan musabbabin lamarin.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani mutumi da ake zargi ya bude wa mahalarta taron biki wuta, inda aka tabbatat da mutuwar mutum daya.
Abun Bakin Ciki
Samu kari