Abun Bakin Ciki
Yan bindiga sun dasa bam a Maru, wanda ya fashe tare da kashe mutum daya, ya kuma haddasa fargaba a yankunan Dansadau da kewaye kamar yadda bidiyo ya nuna.
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya bayyana jin dadinsa da ganin Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya a 1999 bayan ya fito daga gidan yari.
Yayin da Bola Tinubu ke kasar Faransa, shugaban ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima a bikin birne matar Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom.
Hukumar matasa ta NYSC ta tabbatar da cin mutuncin wata matashiya mai bautar ƙasa a jihar Kwara saboda zargin cewa ba ta yi gaisuwa yadda ya kamata ba.
Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta sanar da rasuwar kakarta a ranar Alhamis. Sadau ta ce marigayiyar ta taka rawa sosai a ginuwar rayuwarsu tun daga yarinta.
Wani magidanci ya koka yayin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da 'ya'yansa hudu ciki har da yaro dan shekara biyu a Kaduna.
Kungiyar tattara bayanan gwaninta watau GWR ta tabbatar da mutuwar mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya, John Tinniswood, yana da shekara 112 da haihuwa.
Matashiya yar TikTok a jihar Sokoto, Hamdiyya Sidi Shareef ta fadi abubuwan da suka faru da ita bayan fitar da wani bidiyo da ake zargin ta ci mutuncin gwamna.
Jami'ar jihar Taraba ta shiga jimami sakamakon rasuwar manyan malamanta har guda uku a tsakanin abin da bai wuce kwanaki uku ba, ma'aikata suɓ fara fargaba.
Abun Bakin Ciki
Samu kari