Abun Bakin Ciki
Kwamishinan Wutar Lantarki na jihar Cross River, Dakta Eka Williams, ya rasu a Abuja, lamarin da ya jefa iyalansa da al’ummar Akparabong cikin jimami.
An binne tsohon shugaban PDP na ƙasa, Bamanga Tukur, a Yola bayan rasuwarsa yana da shekaru 91, yayin da Tinubu da manyan jami’ai suka yi masa jimami.
Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a jihar kan rasuwar Bamanga Tukur, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola.
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar dattijon ƙasa, fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar jihar Gongola, Bamanga Tukur.
Tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Bamanga Muhammad Tukur, ya rasu yana da shekara 91, bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya.
Sarkin Igbesi na jihar Kwara, Oba Moses Oyinloye Iwedunmoye I, ya rasa ransa kwanaki bayan kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar.
Kungiyar yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu (NICASA) ta tabbatar da kashe babban malamin coci, Fasto Taiwo Michael Fakunle a birnin Johannesburg.
Bayanai na ci gaba da kara fitowa kan abubuwan da suka kai ga mutuwar Ibrahim Khalil Dan Shagamu, wani mai sharhi a kafafen sada zumunta da aka yanka a Kano.
Rundunar ’Yan sanda reshen jihar Kaduna ta kama wani mutum kan zargin kashe budurwarsa a karamar hukumar Chikun, ya bayyana fadan da suka yi da ita.
Abun Bakin Ciki
Samu kari