Abun Bakin Ciki
Allah ya karbi rayuwar shahararren mai gabatar da shirin 'Rai Dangin Goro,' Ahmad Isa Koto. An ce ya rasu a birnin Legas bayan fama da doguwar jinya.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa hadimin Gwamna Umaru Dikko Radda na Katsina, Aminu Lawal Custom ya rasu a karamar hukumar Malumfashi.
Tsohon sanatan Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo ya ba Wange David wa'adin awa 72 da ta nemi yafiyarsa kan bata masa suna ko su hadu a kotu domin neman hakkinsa.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya dakatar da shugaban karamar hukumar Akuku-Toru, Otonye Briggs a yau Talata 17 ga watan Satumbar 2024 wata uku da nada shi.
Rundunar tsaro ta bukaci al'umma da su guji yin martani kan lamarin Burgediya janar MS Adamu game da sojan ruwa, Abbas Haruna kan zargin cin zarafinsa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane 36 sun rasa rayukansu yayin halartar bikin Maulidi bayan mummunan hatsarin mota a Lere da ke jihar Kaduna.
Ab tafka asarar miliyoyi bayan gobara ta tashi a kasuwar katako ta Itamaga a Ikorodu da ke jihar Lagos yayin da mutane da dama suka rasa shagunansu.
Akalla ofisoshi shida ne gobara ta kone a hedikwatar ‘yan sandan Sokoto a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba bayan da wuta ta tashi da misalin karfe 5 na safiya.
Ambaliyar ruwa ta raba mutane fiye da miliyan daya da muhallansu a Maiduguri da kewaye. Majalisar Dinkin Duniya za ta kai daukin abinci da samar da matsugunni.
Abun Bakin Ciki
Samu kari