Abun Bakin Ciki
Rundunar 'yan sandan Benue ta kama Abdullahi Usman mai shekaru 23 bisa zargin hannu a kisan Farfesa Gabriel Nyityo da ƙanensa a Makurdi da ke Benue.
Wani bincike ya tabbatar da cewa bidiyon da ake yaɗawa da ikirarin ana sayar da Kiristocin Arewacin Najeriya bayi ya yaudari jama'a, domin ba daga Najeriya yake ba.
Adeniyi Adeyemi ya bayyana shirye-shiryen sa na hadin gwiwa da ICPC bayan Shugaban kasa, Bola Tinubu ya umarci hukumar ta binciki huldar hkumar PFIPC.
Wani ɗan sanda ya mutu, fararen hula uku suka ji rauni bayan harin wasu mahara a Gembu, yayin da karamar hukuma ta sanya dokar hana fita ta dare.
Hukumar Kashe Gobara ta Kano ta ce gobara 30 ta kashe mutane biyar tare da lalata dukiyar Naira miliyan 120 a watan Yuni, yayin da ta ceto dukiyar miliyan 481.
Gwamnatin Tarayya ta yi Allah wadai da kisan wasu 'yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu, tare da neman a gudanar da bincike cikin gaggawa a hukunta masu hannu.
Gwamna Bala Mohammed ya yi alhinin rasuwar tsohon Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza, wanda ya rasu a Abuja bayan doguwar jinya.
Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela, ya rasa 'ya'yansa biyu, Mustapha da Ummi, bayan mummunan hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Azare.
Wasu 'yan Najeriya da suka ƙi barin Afirka ta Kudu bayan wa'adin 30 ga Yunin shekarar 2026 sun ɗauki makamai domin kare kansu yayin rikicin ƙin baƙi.
Abun Bakin Ciki
Samu kari