Abun Al Ajabi
Ƴan sandan Anambra sun kama mutum da nonon mace yayin da suke sintiri a yankin Awada. Rundunar ta kuma ceto direban da sace tare da kwato kayan N9.5m.
Sarkin Ijora ya tuɓe rawanin hakimai shida saboda halartar taron siyasa ba izini ba, yana mai tabbatar da tsarin sarauta da kuma goyon bayan gwamnati mai ci.
Bashir Maniya, tsohon ɗan bindiga da ya tuba, ne ya kashe Kachalla Yellow Danbokolo a yaƙin da suka yi, amma shi ma ya rasa ransa a hannun mayakan Turji.
Gwamna Abdulrazaq na jihar Kwara ya maka tsohon ɗan Majalisar tarayya, Moshood Mustapha, da ɗan'uwansa a kotu kan zargin wallafa bidiyon da zai tunzura jama'a.
An ga wani bidiyo da ke nuna lokacin da aka cire hoton Ganduje daga ofishin APC, biyo bayan murabus dinsa. Bidiyon ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Wani ɗan ƙasar Isra'ila, Avi Warshaviak, ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a Otel ɗin Corinthia Villa da ke Garki a Abuja. An tuntubi ofishin jakadancin Isra'ila.
An gano wani jirgin sama da ya yi hatsari a Alabama ba tare da matuƙi ko fasinjoji ba, lamarin da ya zama abin mamaki da ya sa hukumomi suka fara bincike sosai.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa wani mutumi ya hau katon allon sanarwa a daidai gadar Lado, ya ce ba zai sauko ba sai wasu mutane sun je wurin.
Rahotanni daga unguwar Gwammaja da ke birnin Kano sun nuna cewa almajirai 2 yan asalin Katsina sun mutu sakamakon shan wani sindari a shayi, wasu na asibiti.
Abun Al Ajabi
Samu kari