Abun Al Ajabi
Sarkin Iwo da ke jihar Osun a Kudu maso Yamma a Najeriya, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya yi Allah wadai da masu yada jita-jitar cewa yana shan tabar wiwi.
Dawowar Gwamna Dikko Radda daga kasar waje tare da yada zangonsa a Kaduna ya jawo gunaguni daga jama’ar Katsina, yayin da ’yan majalisa suka nuna masa goyon baya.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Ayamelum, Hon. Bernard Udemezue, ya gamu da fushin majalisar dokokin Anambra, inda aka dakatar da shi na tsawon wata 3.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar fitacciyar yar wasan barkwanci, Nwayi Garri yayin da take wasa a wani taro da matar gwamna ta shirya a jihar Abia.
Majalisar dokokin Benue ta zaɓi Alfred Emberger a matsayin sabon shugaba bayan murabus ɗin Aondona Dajoh, inda ya yi alƙawarin shugabanci na adalci da haɗin kai.
Ali Nuhu ya karyata jita-jitar mutuwarsa da ta karade shafukan sada zumunta. An gano yana nan da ransa cikin koshin lafiya tare da cigaba da harkokin fim dinsa.
Wani mutum mai shekara 50 a garin Bama da ke jihar Borno, ya yanke al'aurarsa bayan tsohuwar matarsa ta ƙi komawa gidansa duk da roƙonsa da aka yi kan lamarin.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Gombe ta sanar da kama matasa da masu laifuffuka da dama har da cafke wani Dagaci bisa zargin aukawa wata yarinya ‘yar shekara 12.
‘Yan sandan jihar Ogun sun kama mutum biyu dauke da kokon kan mutane uku a yankin Ijebu, lamarin da ya janyo tunawa da irin makamancin haka a baya.
Abun Al Ajabi
Samu kari