Abun Al Ajabi
Yayin da ake cikin halin kunci a Najeriya, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ki amincewa da saka kwai a jerin abincin da za a siyar a farashi mai rahusa.
Wani faifan bidiyo ya nuna irin shaukin da wani matashi ya jefa mahaifiyarsa a ciki bayan da ya aika mata kudi a matsayin kyautar watan Ramadan..
Wani bidiyo ya nuna yadda wani dan Najeriya ya ba da himma, ya zage ya daga buhun shinkafa da bakinsa, ta hanyar amfani da hakoransa da Allah ya masa.
A karshe, Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ta tare a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Osogbo bayan kammala gyaran da aka yi na tsawon lokaci.
Wata budurwa ta bayyana jin dadi da yadda ta bude shago a madadin ta kashe kudin wurin yin bikinta. Ta bude shagon siyayya kana ta ce tana jin dadin yin hakan.
Yayin da ake cikin mawuyacin hali, gwamnatin jihar Legas ta sanar da kasuwannin da za a sayi kayan abinci cikin rahusa bayan rage farashin da kaso 25.
Wani direban motar bas ya yi bankwana da duniya lokacin da yake tsaka da tuka wasu dalibai zuwa jami'ar Ilorin (Unilorin) da ke birnin Ilorin a jihar Kwara.
Yayin da ake cikin matsi a Najeriya, wani mai sana'ar POS a jihar Kano, Mohammed Sani ya mayar da makudan kudi har N10m da aka tura masa bisa kuskure.
Yayin da ake shan fama a Najeriya, daliban firamare da sakandare a jihar Ogun sun samu kyautar N10,000 ga kowannensu domin rage radadin da ake ciki.
Abun Al Ajabi
Samu kari