Abun Al Ajabi
Hasashen hukumar NiMet ya nuna cewa za ayi zazzafar rana da kuma tsawa daga ranar Litinin zuwa Laraba a Nijeriya. Wannan lokaci ne na bukukuwan Sallah.
Hausawa suka ce sannu ba ta hana kai wa, sai dai a dade ba a je ba. Matashiyar nan Pelumi Nubi, ta so Nijeriya bayan shafe kwana 68 tana tuki daga Landan.
Dattijon da ya fi kowa shekaru a duniya, Juna Vicente Perez Mora ya rasu a jiya Talata 2 ga watan Afrilu da shekaru 114 a kasar Venezuela bayan fama da jinya.
Cocin Redeemed Christian a jihar Ekiti ya kaddamar da kasuwa na musamman domin siyar da kaya cikin farashi mai rahusa yayin da ake cikin wani hali.
Wata mata ta yi tas da asusun mijinta yayin da ya bayyana ba ta ATM ta yi cefane da shi. Ya bayyana irin kayan da aka siya da kudin wadanda suka jawo cece-kuce.
Ministan ayyuka a Najeriya, Dave Umahi ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai shafe shekaru takwas a karagar mulki kamar yadda ubangji ya fada masa.
Wani uba da dansa sun yi aikin dana-sani, sun hallaka wata mata da aka ce makwabciyarsu ce a wani yankin jihar Ogun, 'yan sanda sun kama su yanzu haka.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake taya Shugaba Bola Tinubu murnar cika shekaru 72 a duniya inda ya kira shi a waya na musamman tare da masa addu'o'i.
Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya biya wa maniyyatan jiharsa Musulmai cikon kudin kumar hajji har N1.9m kan kowace kujera bayan hukumar alhazai ta kara kuɗi.
Abun Al Ajabi
Samu kari