Abun Al Ajabi
Tsohon gwamna, Ayo Fayose ya bayyana cewa maganganun Olusegun Obasanjo sun fusata shi ƙwarai a zagayowar haihuwarsa, har ya ji kamar ya buge shi.
Tsohon Gwamna Ayodele Fayose ya umurci cewa a binne shi cikin makonni huɗu bayan rasuwarsa, tare da barin dukkan al’amuran jana’izar a hannun Gwamnatin Jihar Ekiti.
Wata mata ta bayyana yadda wani mutumin Arewa ya dawo mata da wayarta ta iPhone da ta ɓata lokacin sauka daga keke a kasuwa cikin dabara da gaskiya.
An samu rigima mai zafi a birnin Abuja a yau Talata yayin da sojoji suka hana Ministan Abuja, Nyesom Wike, shiga wani fili da ake rikici a Gaduwa.
Wata mata a kasar Bangladesh ta rasu ta bar kudade masu tarin yawa duk da kasancewarta mai bara tsawon sheakru 40 a rayuwarta ba tare da amfani da kudin ba.
Gwamnatin jihar Oyo ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa za ta kakaba haraji a bukukuwan aure, suna da jana’iza, tana mai cewa labarin ƙarya ne.
Wani maharbi a ƙaramar hukumar Boki da ke Jihar Cross River a Kudancin Najeriya ya harbe mace da kuskure yana zaton biri ne yayin da yake farauta a daji.
Wani mawakin Hausa na gargajiya da tauraruwarsa ta fara haskawa, John Mai Molo ya rasa rayuwarsa bayan ya ci abinci a yankin karamar hukumar Tafawa Balewa.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya ce ya yi kokari wurin kawo ƙarshen yaƙin Gaza da ya daɗe yana addabar yankin, inda aka saki fursunoni daga ɓangarori biyu.
Abun Al Ajabi
Samu kari