Abuja
Jirgin saman kamfanin Air Peace ya yi wata saukar gaggawa bayan samun matsala a sama. Jirgin ya dauko mutane daga Benin na jihar Edo zuwa birnin Abuja.
Rundunar yan sandan Najeriya za ta zaƙulo jami'an da suka azabtar da yaran zanga zanga da aka kulle na tsawon watanni uku a Abuja. IGP ya ce za a yi adalci.
Wasu matasa masu zanga-zanga sun cika hedikwatar kamfanin NNPCL a Abuja inda suka bukaci kawo sauyi tattare da harkokin mai yayin da al'umma ke cikin halin kunci.
azauna wasu sassan babban birnin tarayya Abuja da ke tsarin samun hasken lantarki na 'band A' sun fara neman daukin gwamnatin tarayya wajen rage farashi.
Shahararren dan daudu da aka fi sani da Bobrisky ya tsere daga Najeriya bayan kamun da EFCC ta masa. Bobrisky bai bayyana kasar da ya tafi ba har yanzu.
Shugaban gidan rediyon kare hakkin bil'adama da ke Abuja, Ahmed Isa ya dakatar da shirin Brekete Family saboda bacin rai kan gurfanar da kananan yaran Arewa a kotu.
Lauya mai kare yan zanga zanga ya yi kira ga malamai da yan siyasa kan yaran zanga zanga. Lauyan ya ce wulaƙanta yaran zanga zanga cin mutuncin Arewa ne.
Yayin da ake cece-kuce kan tsare yara ƙanana na tsawon watanni uku, Kungiyar Dattawan Arewa sun yi martani tare da yin Allah wadai kan matakin hukumomi.
Rahoton da muke samu ya bayyana yadda Farfesa Ibrahim Maqary ya ba da kudade domin a yiwa yaran da aka tsare a Abuja jinya kafin tabbatar da sun fito.
Abuja
Samu kari