Abuja
Majalisar Wakilai ta amince da kudirin kafa 'yan sandan jihohi bayan kuri'ar 'yan majalisa 311, yayin da 'yan tsiraru suka fice daga zauren majalisar.
Kotun tarayya ta ƙi sauraron buƙatar Bello Bodejo kan sauya sharudan beli, ta ce ya garzaya wajen alkalin hutun kotu yayin da shari'ar EFCC ke ci gaba.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa mutum uku daurin rai da rai bayan sun amsa laifin hannu a garkuwa da dalibai, malamai da kuma alaka da ta'addanci.
Atiku Abubakar ya kalubalanci ware Naira biliyan 22.15 domin fadoji 106, yana bukatar gwamnati ta bayyana hujjar doka da cikakken bayani kan kasafin.
ICPC ta gano ma'aikatan bogi 908 a hukumomin gwamnatin tarayya, inda rundunar 'yan sanda ta zo kan gaba da mutum 570 da ake zargin suna karɓar albashi.
Ga wasu matakai biyar na yadda za ka dawo da layin MTN da aka rufe saboda matsalar NIN cikin mintuna biyar ba tare da an je ofishin kamfani ko an sha wahala ba.
Ministan Kudi Taiwo Oyedele ya bayyana cewa basussukan Najeriya ba su kai N80trn da ake fadi ba, inda ya zargi yawan lissafi da sake fasalin kudi da haifar da hakan.
Hukumar NIHSA ta gargadi Kaduna da jihohi 16 kan yiwuwar ambaliya daga 21 zuwa 27 ga Yulin 2026 tare da bukatar daukar matakan kariya cikin gaggawa.
Majalisar Wakilai ta gayyaci Nuhu Ribadu tare da bukatar Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana kan badakalar hukumar bogi ta PFIPC da ake kan bincike.
Abuja
Samu kari