Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya dauki matakin kirkirar sabuwar sakatariya ta matasa bayan korafin matasa a Abuja inda ya ke ganin hakan zai hana su zanga-zanga.
Hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su bude layukan da suka rufe saboda rashin sanya lambar NIN. Ta ja kunnen kwastomomi.
Yayin da wasu 'yan kasar nan su ka fara zanga zanga a Neja da babban birnin tarayya Abuja, 'yan majalisa sun sanya ranar da za su yi taron gaggawa.
Wasu matasa sun fara gudanar da zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya a jihar Niger. Matasan sun yi kira ga Bola Tinubu kan dawo da tallafin man fetur.
Kungiyar yarbawa ta Afenifere ta samu baraka tsakaninta, inda aka samu bangarori biyu su na adawa da juna a kan zanga-zangar adawa da manufofin shuganan kasa,.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kafa shingen binciken ababen hawa a titin Keffi-Abuja sa'o'i 24 gabannin fara zanga-zangar tsadar rayuwa.
Kungiyoyin matasan Najeriya sun yi martani ga Nyesom Wike kan amfani da dandalin Eagle Square domin gudanar da zanga zanga. Damilare Adenola ne ya yi martanin.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya fara tattaunawa da matasan birnin domin kakkabe ra'ayinsu na shiga zanga-zanga saboda illarsa.
Fadar shugaban kasa ta fito ta musanta batun wani jawabi da ake cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi inda ya dauki matakan tsuke aljihun gwamnati.
Abuja
Samu kari