Abuja
'Yan Najeriya na ci gaba da tururuwa zuwa kan tituna domin nuna adawarsu kan halin kunci da tsadar rayuwar da aka samu a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta dauki matakin sanya masu daukar nauyin zanga-zanga cikin jerin wadanda ake nema ruwa ajallo. Za a yi caraf da su da sun shigo Najeriya.
A yau Talata 6 ga watan Agustan 2024 Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa zai gana da shugabanin hukumomin tsaron kasar game da zanga-zanga.
Jami'an tsaro sun dira a kan mutanen da suka fito zanga-zangar nuna adawa da halin kuncin da ake ciki a kasar nan. Sun cafke mutum uku a birnin Abuja.
Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama Michael Lenin, daya daga cikin jagororin zanga-zangar 'kawo karshen mummunan mulki' da ake yi a birnin Abuja.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ja kunnen matasan Najeriya da kada su bari a yi amfani da su domin kawo cikas ga mulkin dimojuradiyyar kasar nan.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki matakai domin rage wahalhalun da ake fama da su a kasar nan. Ya ce ya ba jihohi N570bn.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fito ya gayawa 'yan Najeriya dalilinsa na cire tallafin man fetur a jawabin da ya yi kan zanga-zangar da ake yi a fadin kasar nan.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci nuna bambancin kabilanci ba a kasar nan. Ya ja kunnen masu yin hakan.
Abuja
Samu kari