Abuja
Kungiyar kwadagon NLC za ta yi zanga zanga a ranar 17 ga Disambar 2025 a dukkan jihohin Najeriya da Abuja. Za a yi zanga zangar ne saboda sace dalibai a jihohi.
Hukumar NMDPRA ta bayyana cewa amfani da fetur ya ragu zuwa lita miliyan 52.9 a rana a Nuwamba, raguwar da ta fito daga lita miliyan 56.7 da aka sha a Oktobar 2025.
Ministan Tsaro, Christopher Musa ya yaba da saurin daukar matakin sojojin Najeriya wurin dakile juyin mulkin Benin da aka yi yunkurin yi a karshen mako.
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce EFCC ta tsare shi ba tare da bayyana dalili ba bayan soke belinsa duk da cewa ya cika sharuddan da aka gindaya masa.
Majiyoyi sun ce zazzafar muhawara ta kaure tsakanin Sanata Ali Ndume da Adams Oshiomhole yayin tantance sababbin jakadu a Majalisar Dattawa a Abuja.
An bayyana yadda EFCC ta kama Dr. Chris Ngige a gidansa da daren Talata, inda aka tafi da shi cikin kayan barci, kuma ake zargin za a gurfanar da shi kotu yau.
ECOWAS ta nada Dangote a matsayin shugaban farko na majalisar kasuwancinta domin karfafa zuba jari na cikin gida, bunkasa cinikayya da hada-hada a Yammacin Afrika.
Yan Majalisa sun kaure da hayaniya da muhawara mai zafi yayin da aka gabatar da wani kudirida ya nemi a gayyaci gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Rundunar 'yan sanda a birnin tarayya Abuja ta kama wani mutum da ake zargi da cewa zai saye harsashi ya mika wa 'yan ta'adda a jihar Zamfara daga Abuja.
Abuja
Samu kari