Jihar Abia
Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da fara ba da ilimi kyauta har zuwa matakin sakandare daga Janairu 2025, domin inganta ilimi ga dukkanin yara a jihar.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin jami'anta na RRS da ke Abia. Rahoto ya ce 'yan bindigar sun kashe wata mata a harin.
Hukumar zaben jihar Abia, ABSIEC ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka yi inda ZLP da YPP suka lashe kujerun yayin da LP mai mulki ta barar.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya sallami shugaban jami'ar ABSU da ke garin Uturu tare da mataimakansa daga aiki, ya naɗa waɗanda za su maye gurbinsu.
Dan Majalisar Tarayya a jihar Abia, Hon. Alex Ikwechegh ya ce ya yi nadamar zabgawa direban tasi mari inda ya bukaci yafiya daga al'ummar Najeriya.
Sojojin Najeriya sun kama jagoran da ya kafa kungiyar ta'addanci ta ESAN a Imo. Sojojin sun kuma wasu manyan yan ta'addan IPOB a Kudancin Najeriya tare da makamansa.
Kungiyar Kiristoci ta CAN ta yi Allah wadai da saka haraji kan allunan coci. CAN ta ce bai kamata a saka haraji a kan wuraren ibada ba kuma gwamnan Abia ne ya fara.
Gwamnatin jihar Abia ta shirya fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N70,000. Gwamnatin za ta fara biyan albashin a watan Oktoba.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya bukaci matasan Najeriya da su shigo a rika damawa da su a harkokin siyasa. Ya ce bai kamata su gujewa neman mulki ba.
Jihar Abia
Samu kari