Bola Tinubu
Shugaban riko na jihar Rivers, Ibok-Ete Ibas ya sauke dukkan masu mukaman da gwamna Siminalayi Fubara ya nada. Ibok-Ete Ibas ya sanar da haka ne a ranar Laraba.
Gwamnatin tarayya karƙashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta ayyana Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun karamar sallah, ta taya musulmai murna.
A kokarinta na yaki da cin hanci, Majalisar wakilai ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman cire kariya ga mataimakin shugaban kasa da gwamnoni.
Yayin da ake ci gaba da shirye-shirye kan hadakar jam'iyyun adawa, jam'iyyar APC na fuskantar barazanar ficewar manyan 'ya'yanta masu biyayya ga Muhammadu Buhari.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo ya bayyana cewa salon mulkin Bola Ahmed Tinubu abin kunya ne, ganin halin da jama'a ke ciki.
Gwamnonin jihohin Bauchi, Adamawa, Bayelsa, Enugu, Osun, Filato, da Zamfara sun maka Tinubu a Kotun Koli kan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa kasar nan na bukatar a yi mata garambawul.
Kungiyoyin kwadago a Ribas sun yi barazanar tsunduma yajin aiki, inda suka bukaci Shugaba Tinubu da ya janye dokar ta-baci da ta hana a biya albashin ma’aikata.
Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya dura kan shugabannin Majalisar Tarayya kan amincewa da dokar ta ɓacun Tinubu a jihar Ribas.
Bola Tinubu
Samu kari