Majalisar dokokin tarayya
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, zai mika ragamar mulki ga mataimakinsa har na tsawon wata guda. Makinde zai yi hakan ne domin tafiya hutu a wannan lokacin.
Mambobin PDP a majalisar dokokin jihar Taraba sun kai 16 yayin da yan Majalisa 3 daga jam'iyyun NNPP da APGA sun sauya sheka a hukumance ranar Litinin.
A labarin nan, za a ji cewa wasu daga cikin ƴan majalisar Adamawa, Anambra, Bauchi, Borno da sauransu sun yi zaman shekara guda a majalisa babu gudunmawar komai.
Majalisar dokokin jihar Benuwai ta dakatar da mambobinta hudu bisa zarginau da shirya makircin sauke shugaban Majalisar, za su shafe watanni 6 ba tare da aiki ba.
Sanata Wadada ya fice daga jam'iyyar SDP saboda rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinye wa, ya kuma nuna yiwuwar komawa APC tare da goyon bayan Tinubu a 2027.
Babbar jam'iyyar adawa ta kasa watau PDP ta shigar da kara gaban babbar kotun tarayya, ta nemi a bayyana cewa babu kowa a kujerun yan majalisa 4 da suka koma APC.
Bayan gudanar da zaben cike gurbi a wasu jihohin Najeriya a ranar Asabar 16 ga watan Agustan 2025 an fara maganar makudan kudi da alawus da za su samu.
Tinubu ya sanya hannu kan dokoki 40 cikin shekaru biyu, ya zarce Buhari da ya sanya wa dokoki 14 hannu. Majalisa ta yaba wa Tinubu kan saurin sanya wa dokoki hannu.
A labarin nan, za a ji cewa 'Dan Majalisar Jiha a Nasarawa, Musa Gude ya nada hadimai 106 domin taimaka masa a harkar gudanar da aikin wakiltar mutanensa.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari