Majalisar dokokin tarayya
An kafa kwamiti da zai yi aiki a Majalisa ya yi bincike kan yadda aka dauki ayyuka a wasu hukumomi. Za a gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin makonni hudu.
Majalisar wakilan Najeriya ta yi fatali da ƙudurin da ya nemi a yi wa wasu sassa na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 kwaskwarima saboda ya saba da tsarin da kasa.
Yan majalisa sun amince da karya farashin abinci. Za a cigaba da karya farashin abinci a jihar Sokoto bayan amincewar majalisar dokoki, za a sayar da abinci da araha
Bankin CBN ya yi matsaya kan amfani da tsofaffin kudi a Najeriya. CBN ya ce za a cigaba da amfani da tsofaffin kudi kuma ba maganar cewa za a canja kudi a Najeriya.
Sanatoci da dama da suka hada da Yahaya Abdullahi (PDP, Kebbi ta Arewa), sun bayyana damuwarsu kan tsakuro kudaden jihohi domin gudanar da a ayyukan hukumomin.
Tsohon dan Majalisar Tarayya a Kwara, Hon. Aliyu Ahman- Pategi wanda ya wakilci mazabar Edu/ Patigi a jihar na tsawon shekaru 12 ya riga mu gidan gaskiya.
Majalisar dattawan kasar nan ta ce ana kokarin daukar hukunci a kan iyayen da ba sa sanya yaransu a makaranta, za a bijiro da kudurin daure iyaye ma watanni shida.
Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya wadatar da sababbin takardun Naira tare da fara janye tsofaffin gabanin 31 ga watan Disambar 2024.
An fara farin ciki yayin da majalisar tarayya ta fara yunkurin samar da sabuwar jiha a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Kudurin ya tsallake karatu na biyu.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari