Majalisar dokokin tarayya
Kudirin dokar da ke neman hana 'yan sama da shekaru 60 yin takarar kujerar shugabancin kasa da gwamna ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa ta samu cikakkun bayanan mutanen da ke son a tsige Sanata Natasha Akpoti Uduaghan daga majalisa.
Majalisar wakilai a yau Laraba 26 ga watan Maris, 2025 ta amince da kudirin dokar da zai mayar da kananan hukumomi a jihar Lagos guda 57 daga 20.
Majalisar Dattawan Najeriya ta ba da umarnin gudanar da bincike kan farashin kuɗin data da kamfanonin sadarwa suka kara wanda ya jefa matasa cikin ƙunci.
A kokarinta na yaki da cin hanci, Majalisar wakilai ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman cire kariya ga mataimakin shugaban kasa da gwamnoni.
Yayin da ake ta kokarin kirkirar sababbin jihohi a Najeriya, Majalisar Wakilai ta amince da karatu na biyu na kudirori hudu da ke neman kan lamarin a Abuja.
Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya kauracewa ambaton Aminu Bayero da “Sarkin Kano” a Calabar, lamarin da ya jawo cece-kuce kan rikicin masarautar.
Kwamitin da majalisa ya kafa kan sauraron korafi game da Sanata Natasha Akpoti ya yi watsi da korafin a bisa dalilin cewa lamarin na gaban kotun tarayya.
Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu wa kudirin mayar da zaben gwamnoni da shugaban kasa rana 1 a Najeriya. Ana sa ran za a fara aiki da shi a 2027.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari