Majalisar dokokin tarayya
A labarin nan, za a ji cewa Majalisar Wakilan Najeriya ta bayyana bukatarta ga Shugaba Bola Tinubu game da dakatar da dokar haraji da ake shirin fara aiwatarwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kadu bisa rasuwar yan majalisar dokokin Kano biyu rana guda, ya ce wannan jarabawa ce ga imani kuma mai wahalar jurewa.
Sanata Ali Ndume ya bukaci Tinubu ya dakatar da aiwatar da sabuwar dokar harajin 2026 sakamakon zargin sauye-sauyen da aka samu a takardun dokokin da aka fitar.
Kasafin kudin 2026 na Naira tiriliyan 58.47 wanda Shugaba Tinubu ya gabatar ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa bayan doguwar muhawara.
Tsohon dan Majalisar tarayya daga jihar Ribas, Hon. Ogbonna Nwuke ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da motarsa ta kama da wuta a birnin Fatakwal.
‘Yan majalisar wakilai shida da suka fito daga jihar Rivers sun sauya sheka daga PDP zuwa APC, lamarin da ya kara raunana jam’iyyar PDP a majalisar tarayya.
A labarin nan, za a ji 'dan majalisar Kaduna ya Arewa, Bello El-Rufa'i ya bayyana dalilin sake fitar da kudi domin daliban Kaduna da ke karatu a KADPOLY.
Wasu 'yan majalisu fuskanci barazanar kiranye daga wajen mutanen da suke wakilta. Kiranyen dai na zuwa ne sakamakon rashin gamsuwa da wakilcin da suke yi.
Jam'iyyar PRP ta yi kira da a tsige shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu matukar aka gano da hannunsa a canza dokokin haraji bayan Majaliaa ta amince da su.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari