Majalisar dokokin tarayya
Kungiyar kwaɗago ta kasa watau NLC ta sake nanata kiranta ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan kudirin sauya fasalin hataji, ta buƙaci a janye shi daga Majalisa.
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan kudirin haraji, Dan Majalisar NNPP daga Kano, Dr Mustapha Ghali, ya ce Najeriya ba ta shirya don aiwatar da dokar gyaran haraji ba.
Dan majalisar Kano, Dr. Mustapha Ghali ya ce bai dace takwarorinsa daga Arewa su zuba idanun a kan kudirin harajin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar masu ba.
Majalisar dattawan kasar nan ta bayyana cewa ma'aikatu da hukumomin gwamnati za su fara bayyana don kare kasafin kudinsu a gabanta kafin aincewa da shi.
Wike ya shirya karbar makudan kudi daga mamallaka filaye a Abuja. Za a tatso biliyoyin Naira daga masu matsala da takardar mallakar kadara a Maitama.
Sanata Ali Ndume ya ji dadin sakamakon adawa da kudirin haraji domin inganta rayuwar jama'a. Ya bayyana cewa an fara samun sakamakon da ake bukata.
Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudden Abbas ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa game da kwace masa fili a Abuja inda ya ce ko sisin kwabo ba a binsa.
Bayan kwace filayen Muhammadu Buhari da yan siyasa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da wa'adin mako biyu ga wadanda abin ya shafa da su biya kudin da ake bukata.
Tsohon shugaban majalisa, Yakubu Dogara ne ya bayyana haka. Ya shawarci 'yan Arewa jagororinsu ne su ka gaza a shekaru 40 da aka shafe ana mulkin kasar.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari