Yan ta'adda
Gwamnatin Donald Trump tana nazarin kai harin soji kan ƙungiyar JNIM mai alaƙa da al-Qaeda a Mali domin ɗakile ta'addanci a yankin Yammacin Afirka.
Khamis Musa Darazo ya bukaci a daina siyasantar da tsaro, ya yabawa Ministan Tsaro Christopher Gwabin Musa tare da neman hadin kan 'yan Najeriya.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce wani harin jirgi mara matuƙi a Kila Bariya ya kashe sama da ’yan ISWAP 20 tare da lalata babura sama da 30 da ma’ajiyar abinci.
Wasu 'yan bindiga sun sace fiye da mutum 50 a Garin Idi da ke Sokoto, sun karɓi N600,000 kafin su sake su, sannan suka kakaba wa al'umma biyan karin Naira miliyan 1.
Sojojin Najeriya sun hallaka babban mai ɗaukar bidiyon Boko Haram, yayin da ƙungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarsa a wani sabon faifan bidiyo da ta fitar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan jagorancinsa wajen yaƙi da ’yan ta’adda, yana mai cewa Amurka za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Najeriya.
Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi magana kan batun cewa ya yi murabus daga mukaminsa. Ya bayyana mutanen da ke fadin hakan.
Dakarun Operation HADIN KAI sun kama wani ɗan Sudan da wasu mutum uku da ake zargi da taimaka wa kungiyar ISWAP, tare da ƙwato kayayyaki a Borno da Yobe.
Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa kwamandojin kungiyar Ansaru biyu, Abubakar Abba da Mahmud Usman, hukuncin daurin rai da rai kan laifukan ta'addanci 32.
Yan ta'adda
Samu kari