Yan ta'adda
'Yan ta'addan ISWAP sun firgita sun sauya wajen zama a Borno bayan rade radin jin cewa jiragen sojojin Amurka sun yi sintiri a yankin Tafkin Chadi a Borno.
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a sabon cocin da aka gina kwanakin nan a garin Ejiba, da ke karamar hukumar Yagba West, inda mazauna suka shiga firgici.
'Yan bindigar da suka sace babban basarake a jihar Kogi, Oba Kamilu Salami sun kira iyalinsa da safe, suna neman N150m kudin fansa kafin su sake shi.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya nuna damuwa kan matsalolin rashin tsaro a Arewacin Najeriya. Ya ce lissafo abubuwan da ke rura wutar matsalar.
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya gana da Bola Tinubu a Abuja domin tattauna matsalolin tsaro da cigaba, tare da godewa gwamnati kan ceto daliban GGCS Maga.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun yi artabu da wasu 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno. Sojojin sun kashe 'yan ta'adda masu yawa.
’Yan bindiga sun saki mutum 37 a karamar hukumar Bakori a jihar Katsina, bayan shafe makonni ana sulhu da miyagun ba tare da biyan kudin fansa ba.
Dan takarar shugaban kasa a LP a 2023, Peter Obi ya ziyarci tsohon ministan Buhari, Chris Ngige bayan 'yan ta'adda sun kai masa hari sun kashe wata mata.
Primate Elijah Ayodele ya ce akwai manyan mutane biyar da ke bayan ta’addanci a Najeriya, yana gargadin gwamnati ta dauki mataki kafin lamarin ya tsananta.
Yan ta'adda
Samu kari