Yan ta'adda
Fiye da mutum 316 sun mutu tun bayan ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a Najeriya. Hare-hare sun karu, lamarin na jefa al'umma cikin alhini mai tsanani.
Wasu kauyuka a jihar Kwara sun bayyana cewa sun samu wasikun 'yan bindiga na cewa za su kai musu hari. Rundunar 'yan sanda da DSS sun samu wasikar.
Wani hari da ake zargin ‘yan bindiga ne ya yi ajalin DPO, CSP Muhammad Sani Sagir, a karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina ranar Juma’a 13 ga watan Fabrairun 2026.
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi martani kan rahotannin da ke cewa 'yan ta'adda sun yi garkuwa da daya daga cikin mambobinta. Ta ce labarin kanzon kurege ne.
Sojojin Najeriya sun ceto wasu mutane takwas da aka sace a wajen biki a jihar Kano. 'Yan bindiga sun saka kayan sojoji sun sace mutanen a karamar hukumar Shanono.
Dakarun sojojin Najeriya masu yaki da ta'addanci sun samu nasara kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun kwato makamai masu yawa a hannunsu.
Hukumar DSS ta gargadi 'yan sanda kan yiwuwar sabon hari a Gbabe, bayan kisan Woro. Gwamna AbdulRazaq ya kira taron gaggawa don inganta tsaro a Baruten.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya gargadi Musulmi su yi aiki tare wajen dakile rashin tsaro da ke haddasa tashin hankali a Najeriya.
'Yan bindiga sun sace masu ibada 9 a cocin Katolika dake Jihar Benue. Shugaban karamar hukumar Ado LGA da ƴan sanda sun tabbatar da cewa jami'an tsaro sun bi sawu.
Yan ta'adda
Samu kari