Yan ta'adda
Yayin da ake cikin jimami, gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da kisan shugaban MACBAN na Benue, Alhaji Ardo Risku da wani dan uwansa.
Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta saki Nura Idris bayan bincike ya tabbatar ba shi da alaka da Boko Haram, tare da ba shi tallafin Naira miliyan uku.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce hare-haren sojin Amurka da ya amince da su a Najeriya sun taimaka wajen dakatar da kashe Kiristoci da masu ta’addanci ke yi.
Yan bindiga sun kona makarantar firamare da ke Dekara a Borgu bayan sun karɓi harajin Naira miliyan 10 da suka tilasta al’ummomin yankin su biya.
An samu rahoton cewa mutane da ke aiki da Sunday Igboho domin farautar 'yan bindiga sun hadu da fushin 'yan bindiga. An yi wa mutanen Igboho jina-jina.
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi tsokaci kan matslalar rashin tsaro. Uba Sani ya ce 'yan bindiga bai kamata su sake sake samun damar rayuwa ba.
Gwamnatin jihar Kebbi ta nuna damuwa kan bullar wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda. Ta bayyana cewa mambobin kungiyar suna gudanar da ayyukansu a jihar.
Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fadi sunayen mutane da kamfanoni guda tara da ake zargi da tallafawa 'yan ta'adda. An sanya masu takunkumi.
Dakarun Najeriya karkashin Operation Fansan Yamma sun kama mota makare da takalma irin na sojoji a jihar Zamfara. Ana zargin 'yan ta'adda za a mikawa.
Yan ta'adda
Samu kari