Yan ta'adda
'Yan bindiga sun kashe mai garin Kulodo, babban ɗansa da mutum biyar a Bodinga ta jihar Sakkwato, yayin da matasa suka tare hanyar Sakkwato-Jega.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Benue, Farfesa David Salifu, ya rasu bayan harbin bindiga da ya samu a wani hari da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai.
Shahararriyar jarumar fim, Clarion Chukwurah, ta ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, shawara kan matsalar rashin tsaron da ake ci gaba da fuskanta a Najeriya.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan ta'addan ISWAP suka kai a jihar Borno. Sojojin sun kashe 'yan ta'adda tare da kwato makamai.
Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Enduring Peace sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda a Plateau. Sojojin sun kuma kwato makamai a hannunsu.
'Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Sabon Birni a Sokoto, sun sace matan aure, yara kanana ciki har da matar liman, sun harbe dan shekara 10.
Kasar Amurka ta janye yawancin dakarunta daga aikin yaƙi da ta'addanci a Tafkin Chadi, amma za ta ci gaba da musayar bayanan sirri da Najeriya a gaba.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda 1,597, sun ceto mutum 1,516 da aka sace tare da gudanar da ayyukan tsaro sama da 14,000.
Dakarun sojoji na rundunar Operation Udoka da ke aiki a yankin Kudu maso Gabas sun samu nasarar cafke jami'an tsaro da ke safarar makamai ga 'yan ta'adda.
Yan ta'adda
Samu kari