
Yan ta'adda







Bayan Peter Obi ya ziyarci Benue, Gwamnan jihar, Hyacinth Alia, ya ce ba zai iya ba da tabbacin tsaron wanda ya kai ziyara ba tare da izini ba ko waye ne.

Gwamnan jihar Filato ya yi zama da sojoji, 'yan sanda da shugabannin kananan hukumomi kan kashe kashe da ake fama da shi a jihar. Ya ce za su hana kai hare hare.

Bayan shirya yin garkuwa da manyan mutane, wani shahararren dan bindiga, , Chumo Alhaji daga Babanla, ya mutu bayan ya kamu da ciwon farfadiya a Kwara.

Shugaba Tinubu ya bukaci Gamna Mutfwang ya kawo karshen rikicin Filato, yayin da Amnesty ta ce an kashe mutum 1,336 daga Disamba 2023 zuwa Fabrairu 2024.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana ta sanar da cewa ta samu nasarar gano wata kungiya da ke safarar mugayen makaman da ake kera wa a cikin kasar a jihar Kano.

'Yan ta'adda sun kai hari karamar hukumar Bassa a jihar Filato, sun kashe mutane 40. Kiristocin jihar sun fara shirye shiryen yin zanga zanga saboda kashe kashe.

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya koka kan irin barnar da 'yan tavaddan Boko Haram suka yi a Borno. Ya bayyana adadin mutanen da suka kashe.

Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar gano wani mugun shiri da 'yan ta'addan ISWAP suke da shi na kafa sansanonin ta'addanci a jihohin Plateau da Bauchi.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya soki ministan yada labarai, Mohammed Idris, kan kalaman da ya yi dangane da rashin tsaro a jihar.
Yan ta'adda
Samu kari