Mafi karancin albashi
Gwamnan jihar Bayelsa, Diri Douye ya amince da biyan N80,000 a matsayin sabon albashi ga ma'aikata inda ya ce ya tausayawa halin da al'umma ke ciki.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya amince da fara biyan mafi karancin albashin N70,000 ga ma'aikatan jihar. Gwamnan zai ba 'yan fansho kudi.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya bayyana cewa nan gaba jihar za ta iya biyan mafi karancin albashi ga ma'aikata na Naira miliyan daya duk wata.
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati bayan ya karɓi rahoton kwamiti.
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya gana da ƴan kwadago, ya sana da N80,000 a matsayon sabon albashin mafi karanci da za a biya ma'aikata a jihar Neja.
Kungiyoyin ma'aikatan kananan hukumomi da malamai a jihar Kebbi sun shawarci Gwamna Nasir Idris ya jinkirta biyan mafi ƙarancin albashi da ya yi niyya.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Ndabuisi Mbah ya amince da sabon mafi karancin albashin da zai rika biyan ma'aikatan jihar. Zai fara aiki daga watan Oktoban 2024.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamna Umo Eno ya amince zai biya sabon albashin N80,000.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan ya amince zai biya ma'aikatan fiye da N70,000.
Mafi karancin albashi
Samu kari