Mafi karancin albashi
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sha alwashin cewa zai maye gurbin duk ma'aikacin da bai fita aiki ba na tsawon kwanak uku saboda yajin aikin NLC.
Yan kwadago sun daidaita da gwamnatin Cross River wajen karin albashi zuwa N7,000. Lamarin ya zo ne a lokacin da yan kwadago ke shirin fara yajin aiki a jihar.
Ƙungiyar NLC reshen jihar Sokoto ta fasa shiga yajin aikin da aka shirya gudanarwa kan mafi karancin albashin ma'aikata. Ta ce ta gamsu da shirin gwamnati.
Kungiyar kwadago reshen jihohi akalla shida sun sanar da janyewarsu daga yajin aikin da NLC za ta shiga a jihohin da ba a fara biyan sabon mafi karancin albashi ba.
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya amince a biya ma'aikatan jihar albashi na watan 13. Gwamnan ya kuma amince da daukar aiki ga wadanda suka kammala karatu.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikata. Gwamna Radda zai rika biyan albashin N70,000.
Gwamnatin jihar Osun ta sanar da cewa ma'aikata za su fara cin gajiyar sabon mafi karancin albashi na N75,000 daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.
Gwamnatin jihar Kaduna ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N72,000 ga ma'aikatan jihar a watan Nuwamba. Gwamnati na jiran koke daga ma'aikata.
Gwamantin Jigawa ta ayyana N70,000 a mafi ƙarancin albashi. Za a rika ba ma'aikata bashin suna noma tare da rage musu farashin kayan abinci a shaguna.
Mafi karancin albashi
Samu kari