Mafi karancin albashi
Abba Kabir Yusuf zai sanar da mafi karancin albashi da zai rika biya a jihar Kano. Abba ya karbi rahoton kwamitin karin albashin ma'aikatan jihar Kano.
Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi ya kafa tarihi bayan shekaru 20, ya amince da karin alawus na N10,000 ga dukkan masu kataɓar fansho a jihar.
Gwamnatin jihar Abia ta shirya fara biyan ma'aikatan jihar sabon mafi karancin albashi na N70,000. Gwamnatin za ta fara biyan albashin a watan Oktoba.
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya amince a fara biyan ma'aikatan gwamnatinsa sabon albashi mafi ƙaranci na N70,000 a watan Oktoba, 2024.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya bi layin gwamnan Legas, ya amince da N85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati.
Gwamnatin Bola Tinubu ta yi wa yan kwadago sababbin alkawura kan karin kudin fetur. Gwamnatin Najeriya ta ce za ta tabbatar an yi karin albashi a dukkan jihohi.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce a watan Janairu, 2025, gwamnatinsa za ta fara biyan N100,000 ga ma'aikata a matsaƴin albashi mafi ƙaranci a jihar Legas.
Gwamnatin jihar Lagos ta amince da biyan mafi ƙarancin albashin N85,000 inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce zai kara mafi ƙarancin albashin zuwa N100,000.
Yayin da ma'aikata ke cikin halin kunci a Najeriya, Gwamnatin jihar Delta ta shirya biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 a karshen wannan wata ta Oktoba.
Mafi karancin albashi
Samu kari